Ilimi a Musulunci

Ilimi a Musulunci
Bayanai
Ƙaramin ɓangare na Islamic governance (en) Fassara da Karantarwa

Iimi ya taka muhimmiyar rawa a Musulunci tun farkon addini, saboda kasan cewar sa tsakiyan nassi da nazarin sa a al'adar Musulunci. Kafin zamani, ilimi zai fara tun yana ƙarami tare da karatun Larabci da Alqur'ani. A farkon ƙarni na farko na Musulunci, tsarin ilimi gaba ɗaya bai zama na yau da kullum ba, amma tun daga ƙarni na 11 zuwa na 12, masu mulki suka fara kafa cibiyoyin ilimi na addini da a kafi sani da madrasa, a ƙoƙarin neman tallafi da haɗinkan malamai (na addini). Bada daɗewa ba makarantun Islamiyya sun yawaita a duk faɗin duniyar Musulunci, wanda hakan ya taimaka wajen yaɗa ilimin addinin Musulunci fiye da birane da kuma haɗakan al'ummomin Musulunci daban-daban wajen gudanar da aikin al'adu tare. Madrasas sun sadaukar da kansu musamman don nazarin shari'ar Musulunci, amma kuma suna bada wasu darussa kamar tauhidi, likitanci, da lissafi.[1] Tarihi ya nuna cewa musulmi sun gada daga wayewar zamani kafin zuwan Musulunci, kamar falsafa da likitanci, waɗanda suka kira “ilimin magabata” ko “ilimi na hankali” daga ilimin addinin Musulunci. Ilimin kimiyya na tsohon nau'in ya bunƙasa tsawon ƙarni da yawa, kuma watsu warsu ta zama wani ɓangare na tsarin ilimi acikin Islama na gargajiya da na da. A wasu lokuta, cibiyoyi irinsu House of Hikima a Bagadaza suna tallafa musu, amma sau da yawa ana watsasu ta hanyar koyarwa daga malami zuwa ɗalibi.[2]

  1. Empty citation (help)
  2. Cite error: Invalid <ref> tag; no text was provided for refs named berkey-ed

© MMXXIII Rich X Search. We shall prevail. All rights reserved. Rich X Search